<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 KORUS
 Aike da abincinka, a bisa ruwaye,
 Gama za ka same shi, bayan ƴan kwanaki.
 (2x)

[V2]
 1) Ga wasu bayi uku, aka yi kiransu,
 Ubangijinsu ya damƙa, masu dukiyarsa.
 Ga wani talent biyar, ga wani talent biyu,
 Ga wani talent ɗaya, gwalgwadon kowa.
 (Solo: &quot;Ɗan'uwa.&quot;)
 Korus

[V3]
 2) Bawa mai talent biyar, da mai talent biyu,
 Suka fidda tsoro, suka yi bangaskiya.
 Suka jujjuya kuɗin, suka sami riɓa,
 Ubangijinsu ya sa, masu albarka.
 (Solo: &quot;Ƴar'uwa&quot;)
 Korus

[V4]
 3) Bawa mai talent ɗaya, shi kuwa ya ji tsoro,
 Ya yi haƙi a ƙasa, ya ɓoye talent nan.
 Ubangijinsa ya ce, kai mugun bawa,
 Ku jefa cikin, baƙin duhu.
 (Solo: &quot;Duka&quot;)

[V5]
 Korus
 4) Ƴan'uwa mu yi koyi, da mai talent biyar,
 Mu fidda tsoro, mu yi bangaskiya.
 Mu aike da abincinmu, a bisa ruwaye,
 Gama za mu same shi, bayan kwanaki.
 Korus</lyrics>
<title>Aike da Abincinka LW353</title>
<hymn_number>353</hymn_number>
</song>